Sin ta fitar da tsarin tabbatar da tsaron fasahar AI
2024-09-10 13:42:31 CMG Hausa
Kasar Sin ta fitar da wani tsarin tabbatar da jagorantar tsaron fasahar kirkirarriyar basira ta AI, yayin babban taron makon tsaron intanet na kasar Sin dake gudana a Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.
Kwamitin kwararru na kasar Sin kan tsaron intanet (TC260), wanda hukumar daidaitawa da tafiyar da harkokin kasuwa ta kasar ta kafa ne ya fitar da tsarin. Tsarin ya kunshi ka’idoji tafiyar da tsaron AI, kamar yadda zai dace da ayyuka bisa hikima, domin tabbatar da tsaro da takaita haddura domin ba da damar tafiyar da shi yadda ya kamata, da bude kofa ga hadin gwiwa wajen jagorantar ayyukan da suka shafi AI.
Bisa yanayin tsarin AI, tsarin ya nazarci hanyoyi da nau’ikan hadduran da suka shafi AI, da gabatar da matakan shawo kansu, da na kandagarki da dakile barazanar tsaro yayin amfani da AI, tare da ka’idojin rayawa da amfani da AI cikin aminci.
Har ila yau, tsarin zai saukaka shigar da jama’a da samun nasarar jagorantar tsaron AI. Haka kuma zai taimaka wajen samar da muhalli mai aminci da adalci na rayawa da amfani da fasahar AI. (Fa’iza Mustapha)