Manyan kwamandojin soji na kasar Sin da Amurka sun yi zantawa ta kafar bidiyo
2024-09-10 21:15:42 CMG Hausa
Bisa matsayar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a taronsu na San Francisco, kwamandan rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin na yankin kudancin kasar Wu Yanan, a yau Talata, ya gana da kwamandan rundunar Indo-Pacific ta Amurka Samuel J. Paparo, ta kafar bidiyo, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi mai zurfi kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu. (Yahaya)