logo

HAUSA

Sin da Amurka sun yi taro kan inganta ayyukan tinkarar sauyin yanayi

2024-09-09 13:42:57 CMG Hausa

Kwamitin inganta ayyukan tinkarar sauyin yanayi a shekarun 2020 na Sin da Amurka ya gudanar da taro na biyu daga ranar Laraba zuwa ta Juma’a na makon jiya a nan birnin Beijing don ci gaba da tattaunawa kan tinkarar matsalar sauyin yanayi.

Ma'aikatar kula da muhalli ta kasar Sin ta bayyana a jiya Lahadi cewa, wakilin musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Liu Zhenmin, da babban mashawarcin shugaban kasar Amurka kan harkokin sauyin yanayi John Podesta ne suka jagoranci taron tare.

A cikin tattaunawar, akwai batun aiwatar da tsarin gudunmawar kasa da kasa na 2030 kan sauyin yanayi ko NDC a takaice, da shirye-shiryen 2035 na NDC. Yayin da bangarorin biyu suka yi musaya ta fasahohi da manufofi wandada aka gudanar ya zuwa yanzu a karkashin kwamitin din, gami da tattaunawa kan sauyin makamashi, da sinadarin methane, da tattalin arzikin madauwari da ingancin albarkatu, da kuma larduna ko jihohi da biranen masu karancin hayaki carbon kuma masu dorewa, kana sun yi fatan ci gaba da tuntubar juna. (Mohammed Yahaya)