An gudanar da jana’izar mutane 48 da hatsarin tankar man fetur ya ritsa da su a jihar Niger
2024-09-09 09:20:46 CMG Hausa
An gudanar da jana’izar mutane 48 wadanda suka rasu sakamakon hatsarin takar man fetur a yankin karamar hukumar Agaye ta jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya.
Hatsarin dai ya faru ne da yammacin jiya Lahadi yayin da tankar man ta yi taho mu gama da motar tirela dake dauke da shanu da matafiya wadda ta taso daga garin Wudil a jihar Kano.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kamar dai yadda darakta janaral na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger Alhaji Abdullahi Baba-Arab ya tabbatarwa manema labarai ya ce, hakika mutane 48 ne suka kone kurmus wanda ta kai ma ba a iya gane su, kuma tun a jiya aka yi jana’izar su a karamar hukumar.
Ya ci gaba da bayanin cewa, hatsarin ta afku ne a kan hanyar Lapai zuwa Agaye, kilomita 2 daga yankin Dendo dake karamar hukumar ta Agaye.
Shugaban hukumar ta SEMA a jihar ta Niger ya kara da cewa, sama da shanu 50 ne suka kone nan take yayin hatsarin da motoci biyun suka yi, sannan kuma wasu kananan motoci guda biyu gobarar ta shafe su.
Ya tabbatar da cewa, tankar man tana makare ne da man fetur.
Ya kara bayyana cewa, hadin gwiwar jami’an bayar da taimakon gaggawa dake hukumar da kuma ’yan kwamitin aikin bayar da ceto na karamar ta Agaye suna ta aikin zakulo sauran gawarwakin jama’ar da suka makale a cikin motocin guda biyu. (Garba Abdullahi Bagwai)