logo

HAUSA

’Yan kasuwa daga kasashe da yankuna 119 sun halarci CIFIT karo na 24

2024-09-08 17:39:20 CMG Hausa

A yau Lahadi aka bude bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin karo na 24 (CIFIT) a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar, wanda aka yi wa taken “Hadewar duniya ta hanyar zuba jari”.

Fadin yankin baje kolin ya kai murabba’in mita 120,000, wanda ya samu halartar ’yan kasuwa daga kasashe da yankuna 119, kuma kusan kashi 80% daga cikinsu sun fito ne daga kasashen da suka hada hannu wajen raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”. (Bilkisu Xin)