logo

HAUSA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin samar da karin kayan aiki na zamani ga `yan sandan kasar

2024-09-08 16:57:59 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kara bayar da himma wajen samar da karin kayan aiki na zamani ga rundunar `yan sandan kasar domin baiwa jami`anta damar gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Ya tabbatar da hakan ne jiya Asabar 7 ga wata yayin bikin yaye dalibai 478 na kwalejin horas da jami`an `yan sanda dake garin Wudil a jihar Kano, ya ce yanzu haka gwamnati tana kan aikin debar `yan sanda masu yawan gaske domin dai kara baiwa matasa damar shiga cikin aikin tabbatar da tsaro a kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya bukaci daliban da aka yaye da su kiyaye sosai da tsarin aiki na zamani wajen gudanar da ayyukansu a duk inda suka samu kansu.

Shugaban ya ce yana da kwarin gwiwar cewa daliban da aka yaye sun samu horo sosai yayin zamansu a kwalejin, wanda zai taimakawa kokarin gwamnati wajen sake fasalin sha`anin tsaro a kasa.

Ya ce babu shakka gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen baiwa kwalejin kulawar da ta kamata a matsayin ta na cibiyar da take yaye jami`an `yan sanda da suka fito daga  kasashen dake yammacin Afrika.

Daga bisani shugaban na tarayyar Najeriya ya kara bukatar sabbin jami`an `yan sandan da su fifita bukatun kasa akan bukatun kansu yayin da suke gudanar da aikin su.

A nasa jawabin, kwamandan kwalejin AIG Sadiq Abubakar ya ce daliban sun samu horo ingantacce a kan dabarun aikin dan sanda wanda tabbas idan suka yi amfani da shi yadda ya kamata, yanayin tsaro a Najeriya zai kara kyautatuwa.(Garba Abdullahi Bagwai)