Kasar Sin da kasashen Afirka sun yi alkawarin ciyar da ayyukan zamanantarwa gaba
2024-09-06 10:24:46 CMG Hausa
A jiya Alhamis ne shugabannin babban taro kan masana’antu da zamanantar da aikin gona na taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024 dake gudana a halin yanzu, karkashin jagorancin ahugaban kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin Wang Huning da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, suka bayyana cewa kasar Sin da kasashen Afirka za su yi aiki tare don ciyar da ayyukan zamanantar da kasashensu gaba.
Inda Wang ya ce, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su tsaya kan hanyoyin bunkasa masana'antu da zamanantar da aikin gona bisa dacewa da yanayi da bukatu na kowace kasa, da sa kaimi ga tabbatar da adalci da daidaici a duniya.
Shugabannin kasashen Afirka a nasu bangare, sun yaba da nasarorin da aka samu a hadin gwiwar kasashen Afirka da Sin a fannonin raya masana'antu, da zamanantar da aikin gona, da sha’anin samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba.
A wannan rana har ila yau, an kuma gudanar da wasu manyan tarurruka da suka shafi hadin gwiwa karkashin shirin “shawarar ziri daya da hanya daya”, da inganta gudanar da harkokin gwamnati, da zaman lafiya da tsaro a nan birnin Beijing. (Mohammed Yahaya)