An gudanar da taron ’yan kasuwa masu kamfanoni na Sin da Afirka karo na 8 a birnin Beijing
2024-09-06 16:09:29 CMG Hausa
A yau, aka gudanar da taron 'yan kasuwa masu kamfanoni na kasar Sin da Afirka karo na 8 a birnin Beijing na kasar Sin.
Sama da wakilan 'yan kasuwa masu kamfanoni na kasar Sin 380 ne suka halarci taron, yayin da aka samu halartar wakilai fiye da 400 na Afirka daga kasashen Afirka 48 da suka hada da Najeriya, Senegal, Afirka ta Kudu, Kenya da dai sauransu. Kamfanonin da suka halarci taron sun hada da wakilai daga masana'antun asali kamar masana’antun makamashi, ma'adinai, kayayyakin more rayuwa, da kuma wakilai daga sabbin masana'antu masu tasowa kamar masana'antun fasahar lantarki, tauraron dan adam na sadarwa, da magunguna.
Taron na 'yan kasuwa masu kamfanoni na kasar Sin da kasashen Afirka shi ne taron koli na tattalin arziki da cinikayya na al'ummomin kasashen Sin da Afirka karkashin tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka. Tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 2003, a kan gudanar da shi a kasar Sin da kasashen Afirka duk bayan shekaru uku. (Mohammed Yahaya)