Wang Yi ya yi bayani game da hadin gwiwar Sin da Afirka da kuma tsakanin Afirka da kasashen duniya
2024-09-06 10:49:49 CMG Hausa
A jiya ne, memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gana da ‘yan jaridar a cikin gida da na waje tare da ministar harkokin wajen kasar Senegal wadda ta jagoranci bangaren Afirka masu halartar dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a wannan karo wato Yacine Fall, da kuma ministan harkokin wajen kasar Jamhuriyyar Congo wanda zai jagoranci bangaren Afirka masu halartar FOCAC a karo mai zuwa, Jean-Claude Gakosso.
Game da hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da kasashen duniya, Wang Yi ya bayyana cewa, yanzu idanun kasashen duniya suna koma kan nahiyar Afirka, da kara maida hankali ga nahiyar ta Afirka. Kuma Sin na jin dadin ganin hakan a matsayinta na abokiyar nahiyar Afirka, kana tana maraba da kasa da kasa su kara nuna goyon baya da taimakawa nahiyar Afirka. Wang Yi ya bayyana cewa, akwai ka’idar musamman kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a dogon lokaci.
Na farko dai, kada a tsoma baki kan harkokin cikin gida na Afirka. Na biyu, a yi la’akari da bukatun bunkasuwa na Afirka. Na uku, kada a yi takarar siyasa tsakanin bangarori daban daban a nahiyar Afirka.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya yi bayani kan hadin gwiwar dake tsakanin Afirka da kasashen duniya, inda ya ce Sin tana fatan kasa da kasa za su cimma ra’ayi daya kan wannan batu. Ya kara cewa, ya kamata a kiyaye adalci, wato Afirka tana da hakkin samun bunkasuwa, wannan ba hakkin ba kebabbe ne ga wasu kasashe. Kana a kiyaye cimma zaman daidai wa daida, wato a saurari ra’ayoyin Afirka a ko da yaushe, da girmama jama’ar Afirka wajen neman hanyoyin samun bunkasuwa da kansu. Hakazalika kuma a yi aiki domin samun moriya, wato ya kamata a yi hadin gwiwa mai amfani don kawo wa jama’ar Afirka moriya. (Zainab Zhang)