Shugabannin Afirka: FOCAC ya zama abun misali mai kyau ga inganta hadin-gwiwar kasashe masu tasowa
2024-09-05 21:00:26 CMG Hausa
An yi bikin bude taron kolin dandalin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka da safiyar yau Alhamis 5 ga watan Satumba, a babban dakin taron al’umma dake Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Senegal dake jagorantar dandalin FOCAC tare da kasar Sin, Bassirou Diomaye Faye, da shugaban kasar Mauritaniya dake jagorantar kungiyar tarayyar Afirka (AU) a wannan zagaye, Mohamed Ould Cheikh Mohamed Ahmed Ghazouani, da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, da shugaban tarayyar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, sun gabatar da muhimman jawabai a wajen bikin.
Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, FOCAC ba dandali da kadai ya taka rawa wajen habaka dangantakar abokantaka tsakanin Afirka da Sin ba ne, har ma ya zama wani kyakkyawan abun misali ta fuskar jagorantar hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ana gudanar da hadin-gwiwar ne daidai bisa sada zumunta, da girmama juna, tare da cimma moriyar juna, kuma kasar Sin na hada kai tare da kasashen Afirka ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba, al’amarin da ya taimaka sosai ga karfafa tuntuba da mu’amalar juna, da habakar tattalin arziki, da kyautatar rayuwar dan Adam a kasashen Afirka. A yanayi mai sarkakkiyar da ake ciki, zurfafa hadin-gwiwa tare da kasar Sin, yana samar da kyakkyawan fata ga kasashen Afirka, na cimma burikan wanzar da zaman lafiya, da zaman karko, da samar da ci gaba mai dorewa.
Shugabannin Afirka sun kuma yaba sosai, tare da nuna cikakken goyon-baya ga muhimmin ra’ayin da shugaba Xi Jinping ya bullo da shi, wato ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, da sauran wasu shawarwarin da suka shafi samar da ci gaba, da tabbatar da tsaro, da raya wayewar kai a duk fadin duniya. Sun ce suna tsayawa tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, da marawa gwamnatin kasar Sin baya wajen kokarin dunkule duk kasa baki daya, da nuna adawa da duk wani yunkuri da aka yi na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin ta hanyar fakewa da batutuwan da suka shafi Taiwan da hakkin dan Adam.
Kaza lika, shugabannin kasashen Afirka suna da yakinin cewa, zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, gami da kara zamanantar da kasa da kasar Sin take yi, zai kara samar da damammakin ci gaba ga kasa da kasa, ciki har da kasashen Afirka. Kasashen Afirka suna fatan aiwatar da nasarorin taron kolin na wannan karo a zahiri, da taimakawa ci gaban sana’o’in zamani, da zamanantar da ayyukan noma, da gina al’ummomin Sin da Afirka bisa kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki, don kirkiro makoma ta zaman lafiya da kwanciyar hankali, da zaman wadata da kuma ci gaba. (Murtala Zhang)