logo

HAUSA

An zartas da sanarwar Beijing da tsarin aiki a taron FOCAC

2024-09-05 14:04:17 CMG Hausa

A taro koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) na shekarar 2024 da aka kaddamar da shi yau Alhamis a birnin Beijing na Sin, an amince da sanarwa kan gina al’ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya daga dukkan fannoni a sabon zamani, wato “sanarwar Beijing” a takaice, da kuma tsarin aiki na taron FOCAC na shekaru uku masu zuwa. (Yahaya)