logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Botswana

2024-09-05 17:48:57 CMG Hausa

A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Botswana Mokgweetsi Masisi, wanda ya zo kasar Sin don halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka a Beijing, inda shugabannin kasashen biyu suka sanar da kafa huldar abokantaka ta manyan tsare-tsare a tsakanin kasashensu.

Xi Jinping ya jaddada cewa, yanzu haka hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka na bunkasa cikin kuzari, wanda hakan ya sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da sauran kasashen duniya, tare da samar da kyawawan sharuda ga bunkasuwar kasashen Afirka. Kasar Sin na son ganin an aiwatar da sakamakon da za a cimma a wajen taron tare da Botswana, don kara amfanawa al’ummar kasashen biyu.

Mr. Masisi a nasa bangaren, ya yaba da jawabi mai burgewa da shugaba Xi Jinping ya gabatar a wajen bikin kaddamar da taron, inda ya sanar da sabbin matakai na tallafawa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen zamanintar da kansu, ciki har da kara bude kofa ga kasashen Afirka, matakin da ya sa kasashen Afirka farin ciki da kwarin gwiwa matuka. (Lubabatu)