logo

HAUSA

Matasan Afrika Sun Yaba Da Nasarorin Da Aka Samu Karkashin Dangantakar Nahiyar Da Kasar Sin

2024-09-04 09:47:11 CMG Hausa

Matasan nahiyar Afrika masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24, sun bayyana amincewarsu ga matakai da nasarorin tafarkin Sin na zamanantar da kanta, tare da jinjinawa irin sakamako na zahiri da aka samu a fannoni daban daban tsakanin Sin da Afrika. Baya ga haka, suna cike da fatan ganin karin ci gaba a nan gaba.

Idan ana batu na tantance hanya mafi dacewa ta samun ci gaba a nahiyar Afrika, al’ummar nahiyar ne ke da hakkin bayyanawa. Kasar Sin ta kasance abokiyar hulda kuma abun dogaro a tafarkin nahiyar na zamanantar da kanta.

Matasan sun bayyana ra’ayoyinsu ne cikin wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN da Jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun cibiyar tuntubar kasa da kasa a sabon zamani, domin jin ra’ayin al’ummar nahiyar Afrika.

Nazarin ya kuma gano cewa, masu bayar da amsar na matukar kaunar kasar Sin. kana daga cikin ra’ayoyinsu kan kasar Sin, kaso 98.7 na ganin Sin a matsayin kasar da ta samu ci gaba.

Ingantaccen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika ya ci gaba da kara kuzari cikin aminci, kuma ya samu yabo daga matasan nahiyar. Kaso 89.8 daga cikin matasan da suka shiga nazarin, sun yi imanin cewa, dangantakar bangarorin biyu ya inganta yanayin tattalin arziki da zaman takewar nahiyar Afrika, kana kaso 90.4 sun yi imanin cewa, jarin kasar Sin ya samar da damarmakin ci gaba ga nahiyar.

Mutane 10,125 daga kasashen Afrika 10 ne suka shiga nazarin. Daga cikinsu, 3,710 wato kaso 36.6, matasa ne masu shekaru tsakanin 18 zuwa 24. Kasashen 10 sun hada da Kamaru da Botswana da Masar da Habasha da Ghana da Kenya da Morocco da Nijeriya da Afrika ta Kudu da Tanzania. (Fa’iza Mustapha)