Xi: Sin da Afirka sun zamo sassa na farko wajen gina al’umma mai makomar bai daya
2024-09-04 21:14:43 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ga mahalarta liyafar maraba, da ya shiryawa manyan baki da suka iso kasar Sin, don halartar taron tattauna hadin kan Sin da kasashen Afirka ko FOCAC na 2024.
A cikin jawabin na sa a yau Laraba, shugaba Xi ya ce a baya da kuma yanzu, Sin da kasashen Afirka sun zamo sassa na farko da suka gina al’umma mai makomar bai daya, kuma tabbas za su hada hannu wajen zama sahun gaba a turbar zamanantarwa a nan gaba.
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, muddin al'ummun Sin da na Afirka biliyan 2.8 sun yi aiki tare, ba shakka za su cimma nasarar samar da sahihiyar hanyar zamanantarwa, da ingiza ci gaban hakan tsakanin kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa, tare da ba da babbar gudummawa ga gina al’ummar bil adama mai makomar bai daya. (Saminu Alhassan)