Masana na kasar Sin da na kasashen waje sun yi musayar ra’ayi kan aikin zamanatarwa irin ta kasar Sin
2024-09-04 16:15:47 CMG Hausa
Masana da kwararru daga sassan duniya sun bayyana ra’ayoyinsu game da zamanantarwa irin ta kasar Sin da tasirinta a duniya, a wani taron karawa juna sani na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Beijing a jiya Talata.
An gudanar da taron na karawa juna sani, wanda ya kasance wani bangare na taron tattaunawa bisa manyan tsare-tsare na Mingde na shekarar 2024, a jami'ar Renmin ta kasar Sin, inda mahalarta taron suka yi tattaunawa kan taken "zamanantarwa irin ta kasar Sin da makomar duniya."
Kwararru a fannin ilimin dabaru bisa manyan tsare-tsare daga kasashen waje, ciki har da na kasashen yammacin duniya, sun bayyana cewa, bisa ga manufar yin gyare-gyare a cikin gida, da bude kofa ga kasashen waje, yunkurin zamanantar da kasar Sin na samun ci gaba cikin sauri, kuma zai kara samar da damammaki ga sauran kasashen duniya. (Yahaya)