logo

HAUSA

Xi ya gana da shugabannin kasashen Libiya da Kamaru da Gabon

2024-09-04 19:13:11 CMG Hausa

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalissar gwamnatin kasar Libiya Mohammed Yunus al-Menfi, da shugaban kasar Kamaru Paul Biya, da shugaban kasar Gabon Brice Clotaire Oligui Nguema, da wasu shugabannin kasashen Afirka, wadanda suka zo kasar Sin domin halartar taron dandalin tattaunawar Sin da Afirka na birnin Beijing.

Haka kuma, uwargidan shugaba Xi, Peng Liyuan ta tattauna, da kuma shan shayi tare da uwargidan shugaban kasar Senegal a birnin na Beijing. (Mai Fassara: Maryam Yang)