logo

HAUSA

Jami'an Afirka da masana sun koyi aikin gine-ginen birane a kasar Sin

2024-09-04 15:07:34 CMG Hausa

A jiya Talata ne jami'ai da malamai 18 daga kasashen Afirka 6 suka kammala wani shiri na ba da horo kan aikin gine-gine da tsare-tsare na birane a kasar Sin.

A cikin kwanaki 14 da suka gabata, an horar da mahalarta shirin daga kasashen Masar, Habasha, Najeriya, Mauritius, Lesotho da Tunisia a Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, da Guiyang, babban birnin lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar.

Wannan shiri na ba da horo, ya baiwa jami'ai da masana na Afirka damar zurfafa fahimtar ayyukan gine-ginen biranen kasar Sin, tare da shimfida hanyar inganta mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wajen raya aikin gine-gine na birane.

Mataimakin daraktan sashen gandun daji na ma'aikatar muhalli ta tarayyar Najeriya Tijjani Zakirai Ahmad, ya ce. "Shirin yana da kyau sosai, mun samu karuwar ilimi sosai, wanda tabbas zai kasance abu mai muhimmanci a gare mu, idan muka koma Afirka za mu yi tunanin yadda za mu aiwatar da abubuwan da muka koya a nan. (Yahaya)