logo

HAUSA

Babban jami’in JKS ya gana da firaministan Nijar

2024-09-04 10:02:25 CMG Hausa

A jiya Talata ne babban jami’in Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin Li Xi, ya gana da firaministan kasar Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine, wanda ke halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024 a nan birnin Beijing.

Li, wanda mamba ne na zaunannen kwamitin harkokin siyasa na JKS, kana sakataren kwamitin ladabtarwa na JKS ya bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta kara inganta fahimtar juna a fannin siyasa da kasar Nijar, da karfafa hadin gwiwa a aikace, da zurfafa mu’amala a dukkan matakai a sassa daban daban, da nufin cimma sabbin sakamako a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare kuwa, firaminista Zeine ya godewa kasar Sin bisa goyon bayan da take nuna wa kasar Nijar, ya kuma ce yana fatan kara zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a dukkan bangarori, da yin aiki tare don rubuta wani sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin kasashen Nijar da Sin. (Yahaya)