logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Sin ya gana da firaministan janhuriyar Nijar

2024-09-03 20:00:21 CMG Hausa

Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gana da firaministan janhuriyar Nijar Lamine Zeine, wanda ya iso kasar Sin domin halartar taron FOCAC na bana.

Yayin zantawarsu a yau Talata, Han Zheng ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Nijar don ingiza alakar su, da hadin gwiwar cimma moriyar juna zuwa sabon matsayi, tare da kara kyautata moriyar al’ummun sassan biyu.

A nasa bangare kuwa, mista Zeine ya ce Sin kawa ce ta gari, kana muhimmiyar abokiyar hulda ga janhuriyar Nijar, wadda kasar ke maida hankali ga hadin gwiwar su a fannin harkokin waje.

Daga nan sai mista Zeine ya godewa kasar Sin, bisa tsawon lokaci da ta shafe tana nuna goyon baya ga Nijar, tare da fatan ci gaba da bunkasa alakar su, da daga matsayi, da gajiyar sakamakon hadin gwiwar sassan biyu a fannoni daban daban. (Saminu Alhassan)