Za a nuna shirin talabijin na gaskiya mai taken "Ciyawar kasar Sin" a tashar CCTV-4
2024-09-03 19:47:51 CMG Hausa
Yayin da ake daf da bude taron FOCAC na bana, an shirya watsa wani shirin talabijin na gaskiya, mai taken “Ciyawar kasar Sin” a tashar talabijin ta CCTV-4, wanda wata kafa karkashin kamfanin CMG ta shirya.
An tsara watsa shirin na "Chinese Grass" ne a gobe Laraba 4 ga watan nan na Satumba. Shirin ya kunshi yadda fasahar Sin ta shuka ciyawar Juncao da ake baiwa dabbobi a matsayin abincin ke kara samun karbuwa, a kasashen Papua New Guinea, da Rwanda da karin wasu kasashen, tare da bayyana labarai game da yadda wannan ‘yar ciyawa ta zamo mai faranta rai tare da amfanar al’ummun kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)