logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da lardin Hebei ta kasar Sin

2024-09-03 09:40:51 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Sanata Uba Sani ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar da wakilan lardin Hebei dake kasar Sin a fannonin da suka shafi ci gaban tattalin arzikin jihar.

Jiya Litinin, 2 ga wata, bangarorin biyu suka sanya hannu a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Wannan hadin gwiwa dai yana kunshe ne cikin sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taron kyautata alakar diplomasiyya tsakanin Najeriya da kasar China.

Kamar dai yadda gwamnan ya fada, za a ci gaba da tuntubar juna akai-akai tsakanin lardin da kuma gwamnatin jihar Kaduna domin dai samar da ci gaba a bangarori da dama dake jihar ta Kaduna.

“Mun karbi bakuncin mataimakin gwamnan lardin Hebei dake kasar Sin, mun kuma sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da ta lardin Hebei a bangarorin da za su taimaki yankunan biyu, kuma yarjejeniyar ta mayar da hankali kan wasu muhimman bangarori, kamar bangaren ma’adanai, aikin gona, kimiyya da fasaha, haka kuma mun duba bangaren ilimi da sauran bangarorin kyautata rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar Kaduna, kowa dai ya san cewa lardin Hebei, lardi ne mai matukar muhimmanci a kasar Sin, wannan ya sanya muku amannar cewa wannan alaka za ta kasance mai amfani ga lardin Hebei da gwamnatin jihar Kaduna.”

A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan lardin na Hebei Mrs Jin Hui ta ce jihar Kaduna jiha ce da take da albarkatun kasa masu yawan gaske kamar nickel, da sinadarin litiyom da kuma gwal, inda ta sha alwashin cewa lardin na Hebei zai tsaya tsayin daka wajen aiwatar da abubuwan dake kunshe cikin wannan yarjejeniya da aka kulla. (Garba Abdullahi Bagwai)