CMG ya sanya hannu kan takardun hadin gwiwa da kafofin NTA da FRCN na Najeriya
2024-09-03 20:18:18 CMG Hausa
Bayan isowar shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu birnin Beijing domin halartar taron FOCAC na bana, tare da gudanar da ziyarar aiki, a yau Talata shugaba Tinubu da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, sun ganewa idanun su sanya hannu kan takardun yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, da babbar kafar talabijin ta Najeriya NTA, da babban gidan radiyo na kasar FRCN.
Shugaban CMG Shen Haixiong, da ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Tuggar ne suka sanya hannu kan takardun hadin gwiwar a madadin kasashen biyu. (Saminu Alhassan)