Xi ya gana da shugaban DRC
2024-09-02 16:06:15 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi jinping ya gana da shugaban jamhuriyar demokradiyyar Kongo (DRC) Felix Tshisekedi, a yau Litinin.
Tshisekedi yana birnin Beijing ne don halartar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024.
Xi ya tuna yadda Sin da DRC suka daukaka dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a watan Mayun shekarar 2023, inda ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da neman samun ci gaba tare da DRC, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin aikin gona, da sarrafa ma'adinai, da koyar da sana'o'i, da kuma ci gaba da taimakawa DRC ta mayar da fa'idar albarkatun kasa zuwa abubuwan da za su bunkasa tattalin arziki.
Xi ya jaddada cewa, a taron kolin FOCAC da za a gudanar, Sin da Afika za su ba da sanarwa game da sabon matsayi na dangantakar Sin da Afirka, da jerin manyan matakai na inganta zamanintar da kai tare, ta yadda za a zana sabon taswira na dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. (Mohammed Yahaya)