logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugabannin Afirka wadanda za su halarci taron FOCAC a birnin Beijing

2024-09-02 14:51:00 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ganawa da shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka ko FOCAC na shekarar 2024, wanda aka shirya gudanarwa tsakanin ranekun 4 zuwa 6 ga watan Satumba a nan birnin Beijing. 

Shugaba Xi ya gana da shugaban Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo Felix Tshisekedi, da shugaban kasar Mali Assimi Goita inda suka bayyana hadin gwiwasu wajen daukaka huldarsu zuwa abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Shugaba Xi Jinping ya kuma gana da shugaban kasar Comoro Azali Assoumani, da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe, da shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, a babban dakin taron jama'a.

Kazalika, Xi zai halarci bikin bude taron na FOCAC, tare da gabatar da muhimmin jawabi a ranar 5 ga watan Satumba, kuma zai shirya liyafar maraba ga shugabanni da wakilan da suka halarci taron.

Bayan taron kolin Beijing na shekarar 2006, da taron kolin Johannesburg na shekarar 2015 da kuma taron kolin Beijing na shekarar 2018, wannan taron da ke tafe shi ma ya kasance wani taron da ya hada 'yan uwa abokan huldar Sin da Afirka. Kuma shi ne taron diflomasiyya mafi girma da kasar Sin ta shirya a cikin 'yan shekarun nan, wanda ya hallara mafi yawan shugabannin kasashen waje. (Mohammed Yahaya)