Shugaba Xi ya zanta da shugaban Afirka ta kudu
2024-09-02 19:01:48 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, yau Litinin a nan birnin Beijing, gabanin taron FOCAC da mista Ramaphosa zai halarta tare da gudanar da ziyarar aiki.
Yayin zantawar ta su, shugabannin biyu sun bayyana daga matsayin huldar kasashen su zuwa cikakkiyar hadin gwiwa bisa matsayin koli daga dukkanin fannoni a sabon zamani. Kaza lika, bayan tattaunawar da suka gudanar, shugabannin biyu sun ganewa idanun su sanya hannu kan takardun wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa masu nasaba da cin gajiyar tsarin tauraron dan adam na ba da jagorancin taswira na Beidou, da gina matsugunan jama’a, da alakar cinikayya, da samar da damar cinikayyar albarkatun gona, da musayar al’adun gargajiya da sauran su.
Har ila yau a dai yau din, shugaba Xi ya gana da shugabannin kasashen Guinea, da Eritrea, da Seychelles da karin wasu kasashen. (Saminu Alhassan)