logo

HAUSA

Adadin fasinjojin da jirgin C919 kirar kasar Sin ya yi jigilarsu ya zarce 500,000

2024-09-02 13:17:23 CMG Hausa

Babban jirgin saman fasinja kirar Sin ko C919, ya kai wani gagarumin matsayi a ranar Lahadi, inda adadin fasinjar da ya yi jigilarsu ya zarce 500,000. 

Tun lokacin da jirgin saman na C919 ya fara jigilar fasinja a ranar 28 ga watan Mayun 2023, jirgin ya yi zirga-zirgar sama da sa’o’i 10,000, kuma ya kammala tafiye-tafiye sama da 3,700 tare da jigilar fasinjoji 500,000.

A ranar 9 ga watan Disamban 2022 ne aka isar da babban jirgin saman fasinja na farko na C919 ga kamfanin jiragen saman China Eastern Airlines. Kuma ya zuwa yanzu, kamfanin ya kara yawan jiragensa na C919 zuwa guda bakwai, inda suke aiki da zirga-zirgar yau da kullum  kan hanyoyi biyar da suka hada Shanghai da Chengdu, Xi'an da Guangzhou da kuma Beijing tare da Xi'an.

Kazalika, a ranar 28 ga watan Agusta, kamfanonin jiragen sama na Air China da na China Southern Airlines su ma sun karbi jirginsu na farko na C919 a birnin Shanghai, lamarin dake alamta yin amfani da babban jirgin saman fasinja na farko da aka kera a cikin gida a sassa da dama, ya shiga wani sabon mataki. (Mohammed Yahaya)