logo

HAUSA

Shugabannin Afirka sun isa birnin Beijing don halartar taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka

2024-09-02 10:44:52 CGTN Hausa

 

Daga daren jiya zuwa sanyin safiyar yau Litinin, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo da na Seychelles Wavel Ramkalawan da na Kongo Kinshasa Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo da na kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, kana da shugaban kasar Afirka ta kudu Matamela Cyril Ramaphosa da firaministan gwamnatin kasar Lesotho Sam Matekane da dai sauransu, sun iso birnin Beijing, don halartar taron kolin dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na shekarar 2024 da za a gudanar a ranekun 4 zuwa 6 a nan birnin Beijing. (Amina Xu)