Wang Yi ya yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta hanyar gudanar da taron FOCAC
2024-09-02 19:49:03 CMG Hausa
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta gabatar da sharhin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ta shafinta na yanar gizo gabanin gudanar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 wato FOCAC, wanda za a yi a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Cikin sharhinsa, Wang Yi ya yi kira ga kasashen Afirka da su hada kansu da kasar Sin, domin amfani da wannan dama wajen inganta ayyukan zamanantar da kasashen Sin da Afirka, yayin da ake tabbatar da gina al’ummun Sin da Afirka masu makomar bai daya.
Ya ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, kasashen Sin da Afirka sun karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa burin neman ci gaba tare, da kuma kare yanayin adalci na duniya ta hanyar yin hadin gwiwa, gami da taimakawa kasashen Afirka wajen neman sulhu ta hanyar yin hadin gwiwa kan harkokin neman zaman lafiya, da kare tsaro, yayin da kuma ake zurfafa zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka ta hanyar kara mu’amala tsakanin jama’ar bangarorin biyu, inda suka kuma cimma sakamako masu gamsarwa da dama. (Mai Fassara: Maryam Yang)