logo

HAUSA

CMG ya watsa shirin talabijin na labaran gaskiya mai taken “Abokai na kusa daga dukkanin nahiyoyi”

2024-09-01 21:21:36 CMG Hausa

Yayin da ake daf da bude taron FOCAC na 2024 a birnin Beijing, an watsa shirin talabijin na labaran gaskiya ta kafafen yada shirye shirye na kamfanin CMG, mai taken “Abokai na kusa daga dukkanin nahiyoyi”.

Shirin wanda kafar CMG ta tsara shi cikin tsanaki, yana kunshe da sakamako daban daban da aka cimma, karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannonin kimiyya da fasaha, da tattalin arziki, da musayar al’adu daki-daki, tare da fayyace labarai daban daban game da cin gajiyar juna, da musayar al’ummu tsakanin sassan biyu, da koyi da juna tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Saminu Alhassan)