An amince Aljeriya ta zama mamba a bankin NDB
2024-09-01 15:49:53 CMG Hausa
A jiya Asabar, bisa agogon wurin, shugabar bankin New Development Bank ko (NDB) Dilma Rousseff, ta bayyana a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu cewa, an amince kasar Aljeriya ta zama mamba a bankin.
Kafin hakan, a watan Yulin shekarar 2023, shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune, ya sanar da cewa, kasarsa ta gabatar da takardar neman zama mamba a bankin na NDB.
Bankin NDB, mai hedkwata a birnin Shanghai na kasar Sin, wani bankin raya kasa ne da kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta Kudu suka kafa tare a shekarar 2015. Manufar kafa shi kuma ita ce tallafawa ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, da na neman ci gaba mai dorewa, a kasashe mambobin kungiyar BRICS, da sauran kasashe masu tasowa, da kuma sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki da na al'umma a dukkanin fadin duniya. (Bello Wang)