CIFTIS na Sin na 2024 zai bunkasa cinikayyar duniya
2024-08-30 20:30:17 CMG Hausa
Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, baje kolin hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin ko CIFTIS dake tafe zai kasance wani muhimmin dandali na zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa, tare da ingiza sabbin hanyoyin bunkasa tattalin arzikin duniya.
Mataimakin ministan harkokin cinikayya na kasar Sin Tang Wenhong, ya ce, baje kolin na CIFTIS na bana, wanda aka shirya gudanarwa a birnin Beijing daga ranar 12 zuwa ta 16 ga watan Satumba, zai ci gaba da mai da hankali kan taken “Hidimomin duniya, samar da wadata tare”.
Sama da kasashe 80 da kungiyoyin kasa da kasa ne za su gudanar da nune-nune a wurin baje kolin. (Yahaya)