Dandalin yaki da ta’addanci na Sin ya tattara ra’ayoyin kasashen duniya
2024-08-30 20:18:44 CMG Hausa
Wani taron kwanaki hudu da aka kammala a yau Juma’a ya hallara wakilai daga sama da kasashe 50, inda suka yi nazari kan sabbin nau’o’in ta’addanci, tare da tattauna kan yadda za a yi amfani da fasahohin zamani wajen yakar ta’addanci.
Sama da mahalarta 300 ne suka tattauna kan “Ayyukan yaki da ta'addanci da fasahohin zamani” tare da cimma matsaya kan batutuwa da dama yayin taron mai taken “Dandalin babbar ganuwa na kasa da kasa kan yaki da ta'addanci na shekarar 2024”.
Avom Nang Jean Jacques, mai kula da harkokin tsaro a ofishin jakadancin Kamaru da ke kasar Sin a yayin bikin rufe taron, ya ce “A wannan dandalin, mun koyi abubuwa da dama.” Yana mai yakinin cewa, tare da hadin gwiwar dukkanin bangarorin, ba shakka za a aiwatar da shawarwarin da aka gabatar a dandalin. (Yahaya)