Sin ta bayyana matsaya game da wasu muhimman batutuwa biyowa bayan ziyarar Sullivan a kasar
2024-08-30 15:57:55 CMG Hausa
Babban darakta a sashen lura da harkokin yankin arewacin Amurka da Oceania a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Yang Tao, ya ce bangarorin Sin da Amurka sun tattauna game da yiwuwar ganawar shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden nan ba da jimawa ba.
Yang ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da ya gudana da yammacin jiya Alhamis, lokacin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida game da sakamakon ziyarar da masharwacin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya gudanar a kasar Sin.
Jami’in ya ce Sin ta shata jajayen layuka 4 masu nasaba da dangantakar sassan biyu, wadanda suka hada da batun yankin Taiwan, da dimokaradiyya da ‘yancin bil adama, da turba da tsarin gudanarwa na Sin, sai kuma batun hakkin Sin na samun ci gaba, yayin da sassa 2 suka gudanar da tattaunawar manyan jami’ai ta baya bayan nan.
Yayin amsa karin tambayoyi, Yang ya ce kamata ya yi Amurka ta gane cewa alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin ta da Sin ta cimma moriyar juna ce, yayin da yunkurin dakile ci gaban tattalin arziki da bunkasar fasahohin Sin, ba abun da zai haifar sai illata ita kan ta Amurka da sauran sassa, kuma yunkuri ne da ba zai yi nasara ba.
Game da batun tekun kudancin kasar Sin kuwa, Yang ya yi nuni da cewa, Sin na nacewa matsayarta ta kare ikon mulkin yankunanta, da hakki da moriyar yankunan tekun ta.
Dangane da batun Ukraine kuwa, Yang ya ce kamata ya yi Amurka ta dakatar da yayata karairayi, cewa wai Sin na goyon bayan sashen masana’antun tsaro na kasar Rasha, ballantana yunkurin amfani da haramtattun matakan kakaba takunkumai na kashin kai. (Saminu Alhassan)