logo

HAUSA

An rike damar dandalin FOCAC wajen raya hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa

2024-08-30 20:05:12 CMG Hausa

A yau ne, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya yi bayani kan dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka a gun taron manema labaru cewa, Sin da kasashen Afirka suna kiyaye zaman lafiya da tsaro da kuma samun bunkasuwa da wadata a duniya. Kana Sin da Afirka suna bin ra’ayin bangarori daban daban, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD, da odar kasa da kasa bisa tushen dokokin kasa da kasa, da kuma ka’idojin raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa kundin tsarin mulkin MDD, da kin amincewa da mulkin mallaka da manufar kama karya.

Lin Jian ya jaddada cewa, Sin da Afirka sun taka muhimmiyar rawa kan tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa da kundin tsarin mulkin MDD da ra’ayin bangarori daban daban da kuma adalci a duniya. Bangarorin biyu za su rike damar taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da za a gudanar a makon gobe don raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa a duniya, da tabbatar da adalci da samun zaman lafiya da ci gaba a duniya baki daya. (Zainab Zhang)