logo

HAUSA

Sin da Afrika sun samu ci gaba mai armashi wajen aiwatar da shawarar BRI

2024-08-29 14:43:44 CGTN Hausa

 

A yau Alhamis ne kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin, ya gabatar da takardar bayani game da ci gaban da Sin da kasashen Afrika suka samu wajen aiwatar da shirin “ziri daya da hanya daya”, wato BRI a takaice na shekarar 2024.

Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa yanzu kasashen Afrika 52, da kungiyar AU sun kulla yarjejeniyoyi tare da Sin karkashin shawarar. Aikin gina manyan ababen more rayuwa na shiga wani sabon mataki, kana kamfanonin Sin sun riga sun shimfida layukan dogo da tsawonsu ya kai fiye da kilomita dubu 10, tare da hanyoyin motoci masu tsayin kimanin kilomita dubu 100, da gadoji fiye da dubu, da tasoshin jiragen ruwa kimanin dari, har ma da layukan wutar lantarki masu tsayin kilomita dubu 66, da ma layukan yanar gizo da sadarwa har kilomita dubu 150.

An gudanar da dandalin hadin kai a fannin yada labarai karkashin shirin “ziri daya da hanya daya” na shekarar 2024, a jiya Laraba a birnin Chengdu na lardin Sichuan, inda aka gabatar da shawarar hadin kai a fannin yada labarai bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”. (Amina Xu)