logo

HAUSA

An bukaci sauran yankunan kasar Sin su inganta shirin karo-karo ga yankin Xizang

2024-08-29 10:30:52 CMG Hausa

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Wang Huning, ya bukaci a samar da ingantaccen tallafi ga yankin Xizang mai cin gashin kansa dake kudu maso yammacin Sin, karkashin shirin karo-karo daga sauran sassan kasar, domin ya cimma burinsa na gina sabon yankin Xizang mai tsarin gurguzu na zamani.

Wang Huning wanda kuma mamba ne na zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bukaci hakan ne yayin taron aiki karo na 4 game da shirin karo-karo ga yankin Xizang.

A bana ake cika shekaru 30 da fara aiwatar da shirin na karo-karo ga Xizang daga sauran yankunan kasar Sin, domin tallafawa yankin.

Da yake jinjinawa nasarorin da Xizang ya samu daga shirin cikin shekaru 30 da suka gabata, Wang Huning ya bukaci a kara mayar da hankali wajen bada taimako bisa tsari kuma mai dogon zango ga yankin, domin daukaka alfanun da aka samu daga shirin. (Fa’iza Mustapha)