Shugaban rundunar sojojin Nijar ya gana da takwaransa na Najeriya a Yamai
2024-08-29 10:04:01 CMG Hausa
A jamhuriyyar Nijar, a ranar jiya ne Laraba 28 ga watan Augustan shekarar 2024, shugaban rundunar sojojin Najeriya janar Musa Christopher ya kai wata ziyarar aiki a birnin Yamai, a daidai lokacin da dangantakar kasashen biyu tsakanin ta shiga wani hali tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Bayan samun tarbo daga takwaransa na kasar Niijar, janar Moussa Salaou Barmou, tawagogin biyu sun shiga tattaunawa ta sa’o’i da dama, da musanya tsakanin sojojin Nijar da na Najeriya, wanda daga karshe wata sanarwar hadin gwiwa ta biyo baya.
Sanarwar ta maida hankali kan yadda kasashen biyu za su maida dangantakar soja domin magance matsalar tsaro da yammacin Afrika yake fuskanta. Haka kuma, shugabannin rundunonin kasashen biyu sun sanya hannu bisa burin zurfafa dangantaka tsakaninsu, da karfafa dangantakar tsaro. Haka zalika, bangarorin biyu sun bayyana muhimmancin tattaunawa da karfafa musanya, da yin aiki tare ta fuskar tsaro, da kuma karfafa dubarun leken asiri tsakanin Nijar da Najeriya, tare da jaddada muhimmancin fadada hulda da ayyukan soja na hadin gwiwa, da musanyar bayanai da daidaita ayyukan soja. A cewar wannan sanarwar, bangarorin biyu sun yi imani da mugun tasirin yaduwar kananan makamai, da kuma imani da saukin samun irin wadannan makamai dake taimakawa wajen kara janyo tashe-tashen hankali, da yake-yake cikin shiyyar, dalilin haka shugabannin sojojin kasashen biyu suka bayyana wajabcin hada karfi da karfe domin kawar da wadannan makamai dake shawagi tsakanin kasashen nasu, da karfafa ayyukan tabbatar da tsaro da yaki da ta’addanci, da kuma bada goyon baya ga kokarin kungiyoyin shiyyoyi da na kasa da kasa ta yadda za’a dakatar da shige de ficen wadannan makamai.
Duk dai a cikin sanarwar, bangarorin biyu sun jaddada karfafa huldarsu da aiki tare domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, kana bangaren Nijeriya ya tabbatar da cewa kasarsa ba za ta hada kai da wata kasa ba domin kawo tashin hankali ko yaki a kasar Nijar ko a wata makwabciyar kasar Nijeriya, a yayin da bangaren Nijar ya dauki niyyar maido da halartarsa wajen aikin hadin gwiwa tare da sojojin Najeriya wajen yaki da ta’addanci. Haka kuma bangarorin biyu sun amince kafa wani kwamitin da zai aiki tare. Daga karshe, shugaban rundunar sojojin Nijar ya amince da goron gayyata na takwaransa a Najeriya domin kammala aikin sabuwar dangantakar soja tsakanin kasashen biyu.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.