logo

HAUSA

An gudanar da taron wayewar kai ta yanar gizo na kasar Sin na 2024 a Chengdu na Sin

2024-08-28 14:36:23 CMG Hausa

Yau Laraba, an gudanar da taron wayewar kai ta yanar gizo na kasar Sin na 2024 a birnin Chengdu dake lardin Sichuan na kasar Sin. Li Shulei, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta Sin (JKS), kana darektan sashen kula da harkokin yada labarai na kwamitin kolin JKS, ya halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi.

Baki mahalarta taron sun yi imanin cewa, karfafa aikin gina wayewar kai ta yanar gizo wani aiki ne da ya wajaba, domin hanzarta daidaitawa da zama dacewa da sabon yanayin bunkasuwar fasahahohin sadarwa mai sauri. Kasar Sin tana mai da hankali kan zamanintar da wayewar kai nau’ika biyu,wato wadanda suka shafi kayayyaki da tunanin mutum, masu dacewa da juna, don haka ta gabatar da babban aikin zurfafa yin gyare-gyare a tsarin al'adu, wanda ke ba da muhimman ka'idoji na ingantawa da raya gyare-gyare a fannin al'adu, da kuma karfafa gina wayewar kai a yanar gizo.

Baki mahalarta taron sun kara da cewa, ya zama wajibi a ci gaba da yada abubuwa masu karfafa gwiwar al’umma a kan yanar gizo, da kuma tabbatar da hadin kan jama’a don ba da gudummawarsu ga aikin gina kasa mai karfi da kuma farfado da al’ummar kasar. (Safiyah Ma)