logo

HAUSA

An bude baje kolin manyan bayanai na kasa da kasa a kasar Sin

2024-08-28 15:30:02 CMG Hausa

An bude baje kolin masana’antar manyan bayanai (Big Data) ta kasa da kasa ta kasar Sin a yau Laraba, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin, wanda ya ja hankalin sama da baki 21,000 da kamfanoni 414 daga ciki da wajen kasar Sin.

Baje kolin na bana mai taken “fasahar zamani na ingiza ci gaban tattalin arziki na dijital” ya mamaye wuri mai fadin murabba’in mita 60,000, kunshe da manyan sassa 6.

Mahalarta sun hada da manyan kamfanoni na cikin gida kamar Huawei da Alibaba da Tencent da Baidu da JD.com da kuma kamfanonin 77 daga kasashe da yankuna sama da 30, cikinsu har da Amurka da Jamus da Canada. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)