Wang Yi Da Jake Sullivan Sun Tattauna Kan Sabon Zagayen Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Kasashen Biyu A Nan Gaba
2024-08-28 21:05:24 CMG Hausa
Darektan ofishin kwamitin koli kan harkokin wajen kasar Sin, kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Wang Yi da masharwacin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro, Jake Sullivan, sun tattauna kan wani sabon zagayen tattaunawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a nan gaba, yayin ganawarsu a birnin Beijing.
Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da aiwatar da muhimman matsaya da aka cimma a taron San Franscisco tsakanin shugabannin kasashen biyu, da ci gaba da yin mu’amala mai zurfi da tuntubar juna a dukkan matakai, da ci gaba da gudanar da hadin gwiwa a fannin yaki da muggan kwayoyi, da tabbatar da doka da oda, da mayar da bakin haure gida, da magance matsalar sauyin yanayi da dai sauransu.
Wang da Sullivan sun kuma amince da su kafa tsarin sadarwa ta kafar bidiyo tsakanin shugabanin rundunonin sojojin kasashen biyu da kuma shirya zagaye na biyu na tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu kan kirkirarriyar basira wato AI a daidai lokacin da ya dace. (Yahaya)