logo

HAUSA

An fara gudanar da babban taro a kan tattara bayanai kan sauyin yanayin da ake samu a Najeriya

2024-08-27 09:19:06 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara gudanar da taron share fage a kan yadda za a tunkari kalubalen sauyin yanayi a jihohin kasar 36, ciki har da birnin Abuja ta hanyar tattara bayanai

A jiya Litinin 26 ga wata ne dai aka fara gudanar da taron a garin Gombe, wanda ya samu halartar  masu ruwa da tsaki wadanda suka kunshi ’yan jaridu da kungiyoyin dake rajin kare muhali da manoma da kuma makiyaya, za kuma a gudanar da makamancin wannan taro a kowace jiha dake fadin  kasar.

Daga tarayyar Najeriya Wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Mr. Jonah Dogo Barde shi ne mataimakin direktan sashen lura da sauyin yanani a ma’aikatar muhalli ta tarayyar Najeriya, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan an tashi daga taron na jiya. Ya ce, duniya ta yi intifakin cewa kasashe masu tasowa dai su ne suka fi fuskantar matsalar sauyin yanayi, duk da cewa kuwa, ba su da hannu a duk wani abu dake kawo dumamar yanayi a duniya.

“Kasashen da suka ci gaba su suke kawo dumamar yanayi, sun fi mu saboda ire-iren ayyukan su amma kuma an gane cewa mu ne wadannan matsalolin ya fi shafa domin ba mu da karfi ko iyawa a kan yadda za mu tunkari sauyin yanayin, don haka duniya gaba daya ta yi zama, kuma ta shirya cewa a taimaki kasashe da suke tasowa domin su cimma burin yadda za su tunkari sauyin yanayi. Yanzu abin da ake ciki shi ne muna tattara bayanai wadanda za su taimaka yadda za mu tunkari wannan babbar matsala. Shi ya sa muke fita muna bi jiha-jiha mu ga kowacce jiha mene ne matsalolin ta domin jihar Gombe misali ba lallai ba ne ya zama daya da na jihar Bayelsa ba, jihar Legos ba lallai ne ya zama daya da jihar Benue ba, saboda haka bayan mun tattara wadannan bayanai za mu saka a cikin kundin guda mu ce ga matsalolin Najeriya ga kuma yadda muke tunanin  yadda za a tunkare ta.” (Garba Abdullahi Bagwai)