logo

HAUSA

Sashen Hausa na CMG ya kaddamar da shirin Kwadon Baka a Nijar

2024-08-27 18:10:53 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 26 ga watan Agustan shekarar 2024 da ta zo daidai da bikin ranar Hausa ta duniya, tawagar babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ta iso birnin Yamai domin kaddamar da shirin kwadon baka da za’a fara nunawa a gidan talabijin da rediyo na kasar Nijar RTN da gidan rediyo da talabijin mai zaman kansa na Dounia da suke watsa shirye shiryensu a Yamai da sauran yankuna na kasar.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Wannan biki ya gudana a gidan Otel Soluxe da ke birnin Yamai tare da halartar manyan jami’an gwamnati, da manyan baki, ‘yan jarida daban daban, da kuma masu sauraren shirye-shiryen sashen Hausa na CMG da ke Nijar.

A lokacin da ta ke gabatar da jawabinta, shugabar tawagar CMG, malama Kande ta bayyana farin cikinta da sake kasancewa a Nijar, da kuma bayyana ma’anar shirin kwadon baka da mahimmancinsa wajen fahimtar kasar Sin a fannoni daban daban da kasancewa wata gada ta karfafa dangantaka tsakanin kasashen Afrika da kasar Sin, musamman ma tsakanin kasar Sin da kasar Nijar. “Shirin kwadon baka, kayatattan shirin talabijin ne da sashen Hausa na CMG ya tsara a kokarin kara fahimtar Hausawa masu kallonmu a kan ainihin kasar Sin da kuma jama’ar kasar Sin daga fannoni daban daban, Hausawa ne masu jagorancin shirin, suna zuwa wurare daban daban domin su ganewa idanunsu wato ci gaban kasar Sin, ganewa idanunsu a kan abubuwa masu ban mamaki da masu ban sha’awa da kuma masu ban al’ajabi. ”

Shugabar tawagar CMG, tana nuna cewa shirin kwadon baka ya samu karbuwa sosai a kasashen Najeriya da Ghana, tana fatan ganin cewa wannan shiri zai samu karbuwa a Nijar.“Mun fara watsa shirin kwadon baka a shekara ta 2021, kuma ya zuwa yanzu mun riga mun watsa shirye shirye fiye da 60, wato a kasashen Nijeriya da kuma Ghana, yau muna farin ciki sosai da ganin yadda wannan shirin zai samu sabbin masu kallonmu daga jamhuriyyar Nijar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, yayin da kasashe biyu suke kulla huldarsu, kyakyawar dangantakar da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu suna da matukar muhimmanci.”

A nata bangare, shugabar sashen kula da sadarwa na ma'aikatar sadarwa da wasiku da tattalin arikin dijitol na Nijar, a cikin jawabinta ta bayyana muhimmancin shirin da kuma yadda zai yaukaka dangantaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu, tare da bayyana fatanta na ganin wannan shirin ya zama abin koyi ga ‘yan jarida a Nijar, in ji madam Chaoulani Aichatou.

“Suna gwada mana gaskiya alakar da ke tsakanin kasar Nijar da kasar China, tana ta kara karfi, a bangaren masu yada labaru yana gwada mana kuma, ‘yan jaridar sashen Hausa na China, da ‘yan jaridar kasarmu gaba daya, ga yadda na gani yana iyar sa cikin kanunmu na ‘yan Nijar mu rinka tunani na bangaren al’adu mu gwadi, mu gwada ma ‘yan Nijar, kowa ya sani kuma duniya gaba daya ta sani. ”

A nasa bangare, sakatare janar din gidan rediyo da talabiji na kasa, Mahamadou Gingarey ya bayyana muhimmancin shirye shiryen CMG a kasashen Afrika da kuma tasirinsu.

“Wannan taro da muke yi, na fari ne muka fara yi a nan tare da Sin, kuma in kun fara kallon talabijin Tele Sahel, kuna ganin kullum ana sa fim da program na Sin, wannan kuma sabo da coorperation wato dangantaka na kasashe biyu suna da kyau.”

Haka kuma shi ma, wakilin gidan rediyo da talabijin na Dounia, malam Kemou Amadou a cikin jawabin nasa, ya bayyana muhimmancin dangantaka tsakanin gidan rediyon nasa da kuma sashen Hausa na CMG tare da bayyana fatan dorewar wannan hulda.