logo

HAUSA

Inganta raya shawarar BRI zai zama daya daga manyan batutuwan da za a tattauna a gun taron kolin FOCAC na bana

2024-08-27 21:06:04 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, nan ba da jimawa ba za a bude taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024, kuma inganta raya shawarar Ziri Daya Da Hanyan Daya wato BRI zai zama daya daga cikin manyan batutuwan da za a tattauna a gun taron kolin.

Game da wannan batu, Lin Jian ya bayyana cewa, a cikin shekaru da dama da suka wuce, a sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, an gina da kuma gyara sabbin hanyoyin motoci wanda tsawonsu ya kai kimanin kilomita dubu 100, da layin dogo fiye da kilomita dubu 10, da gadoji kimanin dubu 1, da kuma tasoshin jiragen ruwa kimanin dari 1 a kasashen Afirka. A halin yanzu, kasashen Afirka 52 da kwamitin kungiyar AU sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwar raya shawarar BRI don yin kokarin samun ci gaba da kansu.

Lin Jian ya ce, Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka wajen yin hadin gwiwar samun moriyar juna da bunkasuwa tare, da hada shawarar BRI da ajandar shekarar 2063 ta kungiyar AU da kuma manufofin kasashen Afirka na raya kansu, ta yadda za a gaggauta sa kaimi ga zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata. (Zainab Zhang)