Sin ta yi watsi da damuwar Amurka game da batun samar da kayayyaki fiye da kima
2024-08-27 11:13:24 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce ficen da kayayyaki kirar kasar Sin suka yi a duniya, sakamako ne na nacewa ga zuba jari a bangaren bincike da amfani da fifikon da kasar ke da shi maimakon jibge kayayyaki masu rangwame da rashin damuwa da yanayin kasuwa ta hanyar aiwatar da matakan kariyar cinikayya.
Lin Jian ya bayyana haka ne lokacin da aka nemi jin tsokacinsa game da wani rahoto da wata kafar yada labarai ta Amurka ta fitar cewa, karuwar jarin kasar Sin a bangaren kera kayayyaki zai ta’azzara batun samar da kayayyaki fiye da kima da matsawa harkokin kasuwanci a duniya tare da kaddamar da wani sabon yakin cinikayya a duniya.
Ya ce bisa kyakkaywan tsarin kera kayayyakin da Sin take da shi, ta taimaka wajen tabbatar da daidaiton tsarin kerawa da samar da kayayyaki da bunkasa ci gaban fasahohi da daukaka ayyukan masana’antu a duniya.
Bugu da kari, ana ganin kasar Sin a matsayin mai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin duniya cikin aminci. (Fa’iza Mustapha)