logo

HAUSA

Zaftarewar kasa ta hallaka mutane 10 a arewacin Habasha

2024-08-26 09:54:08 CMG Hausa

Rahotanni daga arewacin kasar Habasha na cewa, zaftarewar kasa wadda ruwan sama kamar da bakin kwarya ta haifar ta hallaka mutane 10 a gundumar Telemet ta jihar Amhara.

Wata sanarwa da shugaban ofishin gundumar Tesfaye Workneh ya fitar, ta ce yankin na Telemet ya fuskanci mamakon ruwan sama a ranar Asabar wanda ya sabbaba zaftarewar kasa. Baya ga mutanen da suka rasa rayukan su, lamarin ya kuma haifar da mutuwar shanu 35, tare da lalata amfanin gona dake gonakin da fadin su ya kai hekta 30.

Har ila yau, sanarwar ta ce iyalai 480 masu adadin mutane 2,400 sun rasa matsugunan su sakamakon wannan ibtila’i, wanda ya auku yayin da damuna ke kara kankama a Habasha tun daga watan Yuli, ake kuma hasashen ci gaba da saukar ruwan sama har zuwa tsakiyar watan Satumba.

Baya ga yankin arewaci, an kuma samu zaftarewar kasa a kudancin Habasha a farkon watan nan, da karshen watan da ya shude, duka dai sakamakon ruwan sama mai karfi, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar sama da mutane 250. (Saminu Alhassan)