Masaniyar Kenya: Bukatun Afirka ne ke inganta babban fasalin hadin gwiwar Afirka da Sin
2024-08-26 16:11:34 CMG Hausa
Masaniyar tattalin arziki ’yar kasar Kenya Hannah Ryder, ta ce hadin gwiwa tsakanin kasashe da kungiyoyin yammacin duniya da Afirka, ya sha bamban da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, kuma Sin tana yin la’akari da bukatun da kasashen Afirka ke da su, da kuma kwarewarsu sosai, kana abun da ke jagorantar babban fasali na hadin gwiwar Sin da Afirka shi ne bukatun Afirka.
Hannah Ryder ta bayyana hakan ne a yayin da take halartar taron watsa rahoton zuba jari da kamfanonin Sin suka yi a Afirka, kuma taron tattaunawa kan zuba jari a Afirka da aka shirya a Beijing.
Ta ce, hadin gwiwa tare da Sin ba ya bukatar kasashen Afirka su canza manufofunsu na tattalin arziki, a maimakon haka, suna iya gudanar da irin hadin gwiwar da suke so tare da Sin, da kuma wane irin hadin gwiwa za su iya gudanarwa da Sin, ta yadda Sin za ta iya yanke shawarar ba da tallafi kan hakan ko a’a.
Ryder ta kara da cewa, Sin ta taimakawa kasashen Afirka wajen cimma zamanintarwa, da kuma gina manyan ababen more rayuwa a matsayin muhimmin fannin hadin kai. Kazalika, Sin ta gudanar da hadin gwiwar gina manyan ababen more rayuwa, kamar makamashi, da sufuri tare da kasashen Afirka da yawa. Tana kuma fatan a nan gaba Afirka da Sin za su gudanar da karin hadin gwiwa a fannonin raya masana’antun kirkire-kirkire, da sabbin makamashi da sauransu. (Safiyah Ma)