Alhakin karo tsakanin jiragen ruwa a tekun kudancin Sin na wuyan Philippines
2024-08-25 21:00:06 CMG Hausa
Rundunar tsaron teku ta kasar Sin (CCG) ta bayyana cewa, alhakin karu da aka yi tsakanin jiragen rundunar da na Philiippines a yau Lahadi da rana, a yankin tsibiran Nansha Qundao dake tekun kudancin kasar Sin, na wuyan kasar Philippines.
Kakakin rundunar CCG Gan Yu, ya ce jirgin ruwan Philippines mai lamba 3002 ya kutsa yankin ruwan tsibirin Xianbin Jiao na tsibiran Nansha Qundao ba tare da izinin gwamnatin kasar Sin ba, inda rundunar ta dauki matakan da suka kamata a kan jirgin.
Ya ce da misalin karfe 14:12 na yau Lahadi, jirgin ruwan Philippines mai lamba 3002 ya yi biris da gargadi daga bangaren Sin, inda ya yi karo da gangan da jirgin rundunar mai lamba 21551 dake aikin sintiri a lokacin. Kakakin ya bayyana matakin jirgin na Philippines a matsayin mai hadari da nuna rashin kwarewa, lamarin da ya haddasa karo tsakanin jiragen biyu.
Ya kara da cewa, suna bukatar Philippines ta dakatar da keta ‘yancin kasar Sin ko takalarta nan take. Idan kuma ba haka ba, to Philippines ta yi kuka da kanta. (Fa’iza Mustapha)