logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da matakin Amurka na takaita fitar da kayayyakin kasar ga wasu kamfanoninta

2024-08-25 16:22:02 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana adawarta ga matakin Amurka na sanya wasu kamfanoninta cikin jerin wadanda aka takaita fitarwa kayayyaki daga kasar.

Kakakin ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ne ya bayyana haka a yau Lahadi, lokacin da yake amsa tambayar manema labarai game da matakin ma’aikatar kula da cinikayya ta Amurka, na sanya wasu kamfanonin kasar Sin cikin wandanda aka takaita fitarwa kayayyaki daga Amurkar, bisa fakewa da batutuwan da take ikirarin sun shafi kasar Rasha. (Fa’iza Mustapha)