Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da babbar mai shari’a Najeriya
2024-08-24 16:15:27 CMG Hausa
A jiya Juma’a 23 ga wata, shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai rikon mukamin babbar mai shari’a ta kasar.
An gudanar da bikin rantsuwar a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, kuma Kudirat Kekere-Ekun ta maye gurbin mai shari’a Olukayode Ariwoola wanda wa`adin aikinsa ya kare.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Justice Kudirat Kekere-Ekun ta kasance babbar jojin Najeriya ta 23, kuma za ta rike wannan matsayi ne har zuwa lokacin da majalissar dattawan kasar ta amince da nadin nata.
Justice Kekere-Ekun ita ce mace ta biyu a tarihi da suka taba rike wannan mukami a Najeriya bayan Justice Mariam Aloma Muktar wadda ta kasance babbar jojin Najeriya a tsakanin watan Yulin 2012 zuwa Nuwanban 2014.
A jawabin sa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa bangaren shari`a kulawar da ta kamata, a matsayin bangaren na kasancewa babban jigo wajen kyautata tsarin zamantakewar al`umma, tabbatar da bin doka da oda, samar da zaman lafiya da kuma bunkasar tattalin arziki.
“Matsayin babban jojin kasa yana tattare ne da nauye nauye masu tarin yawa a matsayinsa na jagoran duk wasu cibiyoyin shari`a na kasa”
Ya bukaci mai rikon mukamin babban jojin da ta yi kokarin kare mutuncinta da na kasa wajen gudanar da aikinta, domin dai tabbatar da kyakkyawan zaton da ake yi mata.(Garba Abdullahi Bagwai)