logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta bullo da tsarin inshora domin tallafawa manoma

2024-08-23 09:30:18 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukar matakan shigar da tsarin inshorar aikin gona cikin shirinta na bunkasa harkokin noma na kasa domin rage asarar da manoma ke tafkawa tare kuma da tabbatar da kyautata sha’anin samar da abinci.

Karamin minista a ma’aikatar gona Sanata Aliyu Abudllahi ne ya tabbatar da hakan a birnin Abuja ranar 21 ga wata yayin wani taron karawa juna sani na yini uku da aka shirya domin ilimintar da masu ruwa da tsaki a kan alfanun dake tattare da shirin inshora ga manoman Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ministan ya ce, babu shakka wannan yunkuri da gwamnati ke yi zai taimaka wajen rage fargabar da wasu manoma ke nunawa wajen rungumar sana’ar aikin noma gadan-gadan saboda irin dimbin asarar da suke tafkawa sakamakon matsaloli na sauyin yanayi da sauran annobar dake shafar muhalli a wasu sassan kasar.

Ya ce, hakkin gwamnati ne ta kare jarin da take sanyawa a bangaren aikin gona ta hanyar hadin gwiwa da abokan hulda kamar bankin raya kasashen Afrika.

Karamin ministan gonar ya bayyana taron a matsayin wani dandali da zai kara fadakar da manoma dabarun lura da yanayi da zai bayar da damar samun amfani mai kyau, inda ya ce, da yawa wasu manoma ba sa la’akari da yanayi a duk lokacin da suka tashi shuka amfanin gona.

“Duk manomin da yake a yankin da ake fuskantar barazanar ambaliyar ruwa, tuni aka sanar da shi ilimin da zai haska masa lokutan da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa, a don haka bai kamata ma manomi ya yi shuka a irin wadannan wurare ba wanda akwai jahohin da tun kafin faduwar damuna aka sanar cewa za su fuskanci matsalar ambaliyar ruwa a bana.” (Garba Abdullahi Bagwai)